Hukumar Kula da Tsare-tsaren Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta kaddamar da Makon Ƙorafe-Ƙorafe na farkon zangon shekara 2025, a ofishinta na shiyyar Zaria.
Wannan shiri na musamman a tsara shine domin baiwa jama’a dama su bayyana damuwarsu, su yi tambayoyi da kuma ba da shawarwari kan yadda za a inganta tsare-tsaren gine-gine da ci gaban birane a faɗin jihar.
Darakta Janar na KASUPDA, Bldr. Abdurrahman Yahya, PhD, ya jagoranci kaddamarwar, inda ya bayyana cewa wannan mako yana ɗaya daga cikin hanyoyin da hukumar ke amfani da su don kusantar al’umma da kuma karɓar ra’ayoyinsu kai tsaye.
Ya ce: “Mun buɗe wannan dandali ne don jin ƙorafe-ƙorafen jama’a domin ƙarfafa gaskiya da adalci a ayyukan mu.”
Shirin na daga cikin manufar gwamnatin Gwamna Uba Sani na inganta mulkin da jin raayoyin jama’a, inda ake baiwa kowa damar shiga cikin harkokin gwamnati.
KASUPDA na shirin ci gaba da wannan shiri a sauran sassa na jihar domin tabbatar da cewa ba a bar kowane yanki a baya ba.