Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Ko Kun San?

Hukumar KASTRA Ta Samar da Naira 3,000 a Watanni Uku Farko Shekarar 2025

Published

on

Hukumar Kula da Harkokin Sufuri ta Jihar Kaduna (KASTRA) ta samar da naira dubu uku kacal (₦3,000) a matsayin kudaden shiga a watanni uku farko na shekarar 2025, kamar yadda rahoton aiki na kasafin kudin jihar ya nuna.

A cewar kasafin kudin da aka amince da shi na 2025, ana sa ran hukumar KASTRA za ta samar da sama da naira biliyan 30 a matsayin kudin shiga ga jihar cikin shekara daya.

Amma rahoton aiki na farkon kwata (Watanin Ukun Farko) ya bayyana cewa hukumar ta samu kashi 0.0% na kudin da aka sa rai hukumar zata samar a wanna shekarar.

Haka zalika a Shekarar 2025 hukumar zata kashe sama da biliyan 30, sanan alkaluma na nuni da cewa a watanin ukun farko hukumar ta kashe sama da naira biliyan 3 Wanda yayi daidai da kaso 10.8% na adadin kudin da ake sa rai hukumar zata kashe a wanna shekarar.

Bayanin samar da naira 3,000 ya bayyana a cikin karkashin tatara kudi “Revenue by Administrative Classification”na Ministri Ayyuka da Ababen More Rayuwa, mai dauke da lamba 023400700100 a sabon rahoton da aka saki na aiki da kasafin kudin Kaduna na farkon kwata (Watanin Ukun Farko) na shekarar 2025.

Haka zalika bayanin kashe kuɗin hukumar na watan Ukun Farko shima yana karkashin Ministri Ayuka da ababen more rayuwa Mai dauke da lamba 023400700100.

Hukumar KASTRA, an kafa ta ne domin tsara, raya, da kula da dukkan nau’ukan sufuri na jama’a da ababen more rayuwa da ke da alaƙa da su a fadin jihar Kaduna, tana da nauyin tabbatar da tsarin sufuri mai inganci da bin doka.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.