Hukumar Kula da Bayanai na kasa ta Jihar Kaduna (KADGIS) ta karɓi tawagar hukumar makamanciyar ta daga Jihar Taraba wadda ta zo ziyarar ban girma da nufin koyon sabbin hanyoyi na gudanar da aikin zamani.
Shugaban Hukumar Taraba TAGIS, Alhaji Sambo Sunusi, ya bayyana cewa sun zo ne domin koyon yadda KADGIS ke gudanar da tsarin aikin harkan kasa na zamani tare da neman shawarwari kan yadda za su gina ingantaccen tsari da zai taimaka wajen samar da kudaden shiga ga jiharsu.
A nasa jawabin na maraba da baƙin, Daraktan Hukumar KADGIS, Dr. Bashir Garba Ibrahim, ya gabatar da taƙaitaccen bayani game da aikace-aikacen hukumar da yadda take aiki. Ya kuma bayyana wasu daga cikin sabbin hanyoyi da za su iya taimaka wa Taraba wajen kafa tsari mai ƙarfi da kuma samun kudaden shiga.
Tawagar daga Taraba ta zagaya sassa daban-daban na KADGIS inda suka ga yadda ma’aikatan ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
A ƙarshe, tawagar ta nuna gamsuwa da yadda aka karɓe su, tare da tabbatar da cewa za su aiwatar da abubuwan da suka koya a yayin ziyarar domin inganta ayyukan TAGIS a Jihar Taraba.