Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Hon. Munira Tanimu Ta Karbi Bakuncin Masu Shirya Gasar Croccity Basketball, Art And Music Festival

Published

on

Shugabar masu rinjaye a Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, Hon. Munira Suleiman Tanimu, ta tarbi kwamitin shirya bikin Croccity Basketball, Art and Music Festival a ofishinta, inda suka tattauna hanyoyin da za a bunkasa wasanni da fasaha ga matasa a jihar.

Tattaunawar ta mai da hankali ne kan samar da karin damammaki ga matasa domin su bayyana baiwarsu a fagen kwalon kwando, zane-zane da waka. Hon. Munira ta nuna goyon bayanta ga shirin, tana mai cewa:

“Ko da yaushe idan ina cikin irin wannan hira, sai in tuna da rayuwata a Essence International School—inda nake taka kwallo kwando sosai. Kwalon kwando wasa ne da na shaku da shi tun ina ƙarama. Watakila lokaci ya yi da zan koma filin wasa! Lol.”

A yayin taron, an miƙa mata rigar was an kwalon kwando ta gasar a matsayin girmamawa. Hon. Munira ta karɓa cikin farin ciki, tana mai fatan ganin wannan biki ya zama babban dandalin ƙarfafa matasa da ci gaban al’umma.

Croccity Basketball, Art and Music Festival wata babbar gasa ce da ke haɗa wasanni, fasaha da nishadi a lokaci guda, wadda ke baiwa matasa damar bayyanar da ƙwarewarsu a fannoni daban-daban.

A ƙarshe, Hon. Munira ta tabbatar da cewa zata ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen da ke ƙarfafa matasa da bunƙasa cigaban al’adu a Kaduna.

Copyright © 2024 kaduna Reports.