Yar majalisar jihar dake wakiltar jama’ar Lere ta gabas, Hon. Munira Suleiman Tanimu shugaban masu rinjaye a majalisar jihar Kaduna, ta Gabatar da Kudirin Dokar Kafa Kwalejin Kimiyyar Noma da Muhalli ta Saminaka.
A zaman majalisar dokoki ta jihar Kaduna da aka gudanar a ranar litini, an gabatar da muhimman kudirin dokoki da dama wadanda suka samu karatu na farko da na biyu.
A cikin zaman, an gabatar da Kudirin Dokar Kafa Kwalejin Kimiyyar Noma da Muhalli a Saminaka. Kudirin, wanda Hon. Munira Suleiman Tanimu ta dauko, ya samu karatu na farko ba tare da tsaiko ba.
A yanzun haka majalisar ta dage zamanta sai ranar 13 ga watan mayun 2025.