Jaba, Kaduna – A kokarin bunkasa aikin noma da tabbatar da wadatar abinci, Shugabar Karamar Hukumar Jaba, Hon. Larai Sylvia Ishaku, ta kaddamar da Shirin Tallafin Noman Rani a harabar sakatariyar Karamar Hukumar Jaba.
Wannan shiri, wanda aka fara karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, yana da nufin karfafa aikin noma a kowane lokaci na shekara ta hanyar samar da mahimman kayan tallafi ga manoma, musamman kanana. Kayayyakin da aka raba sun hada da taki, injinan ban ruwa, injinan huda kasa (power tillers), magungunan feshi (knapsack sprayers), injinan nika ragowar amfanin gona, da injinan sarrafa ciyawa domin bunkasa samar da abinci da tallafawa al’ummar karkara.
Da take jawabi a wurin taron, Hon. Larai Sylvia Ishaku ta bayyana muhimmancin wannan shiri wajen taimakawa manoma da bunkasa noma a yankin. Ta tabbatar da cewa gwamnatinta za ta ci gaba da bayar da tallafi domin ganin manoman Jaba sun ci gajiyar irin wadannan shirye-shirye.
“Wannan shiri wata babbar dama ce wajen tabbatar da wadatar abinci da habaka tattalin arzikin al’umma. Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa manomanmu suna da dukkan kayan da suke bukata domin bunkasa noma, musamman a lokacin rani,” in ji ta.
Ta kuma yaba wa Gwamna Uba Sani bisa jajircewarsa wajen inganta harkar noma, tana mai jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da kokarin tallafawa manoma da kara yawan amfanin gona a Jihar Kaduna.
Manoma Sun Nuna Godiyarsu Bisa Tallafin da Aka Ba Su
Taron kaddamarwar ya samu halartar jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, da manoma daga sassa daban-daban na Karamar Hukumar Jaba. Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun bayyana godiyarsu ga wannan shiri, suna mai cewa ya zo a dai-dai lokacin da ake bukatarsa.
Wani karamin manomi daga Sab-chem, Malam Bitrus Rangye, ya ce:
“Wannan tallafi daga Gwamna Uba Sani da Hon. Larai Sylvia Ishaku babban taimako ne a gare mu manoma. Da wadannan kayan aiki, za mu iya noma da yawa kuma mu kara yawan amfanin gona ko da a lokacin rani.”
Haka kuma, wata manomiyar kayan lambu daga Chori, Mrs Rahila, ta bayyana jin dadinta da shirin, tana mai cewa:
“Samar da famfunan ruwa da takin zamani zai taimaka mana matuka. Muna matukar godiya ga wannan kokari na gwamnati wajen tallafawa manoma da tabbatar da wadatar abinci.”
Aniyar Ci Gaban Aikin Noma
Shirin Tallafin Noman Rani yana daya daga cikin ginshikan manufofin mulki guda bakwai (7-point agenda) na Hon. Larai Sylvia Ishaku, wanda ke mayar da hankali kan noma a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arziki da bunkasa karkara a Jaba.
Ana sa ran wannan shiri zai inganta noman zamani, rage dogaro da ruwan sama, da tabbatar da wadatar abinci a jihar. Wannan mataki wata babbar nasara ce a kokarin gwamnatin Kaduna na samar da ci gaba mai dorewa a bangaren noma da inganta rayuwar al’umma.