Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Hon. Jafaru Ahmed Ya Jagoranci Taron Tsaro Na Wata A Lere

Published

on

A yau Laraba, Hon. Jafaru Ahmed, shugaban karamar hukumar Lere, ya jagoranci taron tsaro na wata-wata a zauren majalisar karamar hukumar.

Taron ya samu halartan wakilan hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da na al’umma.

A yayin taron, an duba halin da tsaro yake ciki a fadin karamar hukumar da kuma tattaunawa kan matakan ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka.

Shugaban ya yabawa kokarin jami’an tsaro da tsayuwar dakan al’umma wajen kula da tsaro.

“Tsaro alhakin kowa ne. Mu ci gaba da aiki tare cikin hadin kai, tattaunawa da girmama juna,” in ji Hon. Jafaru Ahmed.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.