Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Illimi

Hon. Bello El-Rufai Zai Raba Kayan Makaranta Ga Dalibai 400 a Kaduna North

Published

on

Hon. Mohammed Bello El-Rufai, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna North.

A ci gaba da shirye-shiryen tallafa wa al’umma, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaduna North, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ya bayyana cewa zai raba kayan makaranta ga dalibai 400 a makarantun firamare hudu a mazabarsa.

Wannan shirin, wanda aka saba aiwatarwa tun bayan hawansa kujerar majalisa, an tsara shi ne tare da hadin gwiwar kungiyar masu dinki na Unguwar Sarki (Complex), domin karfafa sana’o’in  na cikin gida.

A cewar dan majalisar, makarantun da za su amfana daga wannan shiri sun hada da:

LGEA, Rafin Guza, Kawo Ward

LGEA, Ali Dogo, Unguwar Shanu/Abakwa

LGEA, Maiduguri Road, Gaji Ward

LGEA, Yusuf Dantsoho, Gabasawa Ward


Ya kara da cewa, an yi tunanin hada da makarantar masu bukata ta musamman (Deaf School) da aka tallafa wa a baya, amma saboda bambancin launin kayan makarantarsu, za a shirya wani shiri na musamman domin su.

Hon. Bello El-Rufai ya ce, za a biya dukkanin masu dinki kudinsu bayan kammala aikin. Don tabbatar da adalci da inganci, za a kafa kwamitin da zai lura da rabon kayan tare da hadin gwiwar shugabannin makarantun da abin ya shafa.

Shugabar kwamitin kula da rabon kayan ita ce Hajiya Fatima Sani One Minute (Mama Na), tare da:

Shugaban kwamitin: Nuhu Sani Lere, Mai Bawa Shi Shawara Kan Ilimi (Doka/Gabasawa)
Mataimakin Shugaban Kwamitin: Jibiril Abdullahi (Belgium)
Mambobi: Comrade Umar Babayo, Najib Wali, Hadiza Musa Gombe, Nafisa Idris, Raveve Bala Goro, AS Sabo, Aminu Namama (Kwamishinan Gaji Ward), Jibiril Isa Maikarfi (Shugaban Unguwar Shanu Ward), Haruna Naibi (Wakilin ‘yan dinki)

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.