Connect with us

Siyasa

Hon. Bello El-Rufai Ya Jika Hanta Abokan Siyasar Sa da Naira Miliyan 32

Published

on

Hon. Bello Elrufai

A jiya, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna North, ya raba tallafin kuɗi na Naira miliyan 32 ga wasu daga cikin abokan siyasar sa. Waɗannan mutanen sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da ya samu a zaɓe, musamman a matsayinsu na mambobi a kwamitocin yaƙin neman zaɓensa.

A cewar Hon. El-Rufai, wannan tallafi wani yunkuri ne na ƙarfafa waɗanda suka ba da gudunmuwa wajen samun nasarar sa, tare da nuna godiya da kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da bai wa al’umma hakkinsu ba tare da la’akari da jam’iyya, addini ko kabila ba.

Yadda Aka Raba Tallafin

A cikin bayanin da ya fitar, Hon. El-Rufai ya bayyana yadda aka rarraba tallafin kamar haka:

Naira miliyan 1.5 ga mutum 10 daga cikin Kwamitin Aiki na Tsakiya.

Naira miliyan 1 ga mutum 6 daga cikin shugabannin kwamitin gundumomi, inda sauran 6 za su karɓi tallafinsu a mataki na biyu.

Naira miliyan 2 ga mutum 4 daga cikin manyan mashawarta, waɗanda ke jagorantar shirye-shiryen da suka shafi mazabar.

Naira dubu 200 ga mutum 12 daga tawagar kafofin watsa labarai.

Naira dubu 500 ga mai ɗaukar hotunan ofishin mazabar.


Hon. El-Rufai ya kuma bayyana cewa an yi tanadin kuɗin marigayi Auwal Shuaibu, wanda ya rasu kwanan nan, domin a bai wa iyalinsa a matsayin tallafi. Ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.

Ya kuma gode wa mashawartansa da abokan aikinsa, ciki har da Mallam Hafiz Bayero, Hon. Muktar Baloni da Mallam Sadiq Yusuf, bisa gudunmuwar da suka bayar wajen wannan shiri.

Hon. El-Rufai ya tabbatar da cewa tallafin na ci gaba ne kuma za a aiwatar da matakin biyu nan gaba domin ƙarin mutane su amfana.

Copyright © 2024 kaduna Reports.