Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya fitar da naira miliyan 2.1 domin tallafawa kungiyar masunta a unguwar Kabalan Doki, me suna Kaduna North Artisanal Fishers Cooperative.
Masu sana’ar kamun kifi sun ce suna fama da matsalolin kayan aiki da kuma karancin tallafi daga gwamnati.
Dan majalisar ya ce kudin zai taimaka wajen saukaka ayyukan masunta, musamman a lokacin damina. Cikin bukatun da kungiyar ta gabatar har da kwale-kwale guda hudu.
El-Rufai ya ce za a saya musu kwale-kwalen da kuma sauran kayan aiki da suka bukata. Ya ce ya kara da naira miliyan daya domin siyan karin kayan aiki.
Wakilan dan majalisar sun gana da shugabannin kungiyar, yayin da shi kuma ya ce ya kira shugaban kungiyar a waya.
Dan Majalisar ya kafa wani kwamitin wucin gadi domin kula da rabon tallafin, kwamitin ya hada da Abubakar Abdullahi Salisu, shugaban APC na Kabala, a matsayin shugaba.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Abdullahi Isa Ajeadawo, Isiya Aliyu Kabala, Shamsu SS Adam, Ashiru Nagoma da Hajiya Hafsat Gwagwada.
El-Rufai ya ce wannan na daga cikin alkawuran da ya dauka lokacin kamfe.