Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Haɓaka Kwarewa da Karfafa Matasa Sune Ginshikan Tattalin Arzikin Kaduna – Dakta Hadiza Balarabe

Published

on

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana cewa habaka kwarewa da karfafa matasa su ne ginshikan tsarin tattalin arzikin Gwamna Uba Sani.

Ta bayyana hakan ne yayin kaddamar da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Maltina da kamfanin Nigerian Breweries PLC ya gina a unguwar Makera Kakuri a matsayin wani bangare na ayyukan al’umma na kamfanin.

“Abin da Nigerian Breweries ta yi a nan ya yi daidai da manufofin Gwamna Uba Sani na bunkasa kwarewa da karfafa matasa da mata don samun dogaro da kai,” in ji Dakta Balarabe, wadda ta wakilci gwamnan wajen kaddamar da cibiyar.

Dakta Balarabe ta bayyana wannan cibiyar a matsayin wata hanya ta ba matasa mafita daga rashin aikin yi, da kuma mataki na samar da sabbin damammaki na tattalin arziki.

“Cibiyar za ta sauya matasa daga masu neman aiki zuwa masu samar da ayyukan yi, ta yadda za su dogara da kansu kuma su bunkasa tattalin arzikin yankinsu,” in ta bayyana.

A cewar ta, gwamnatin jihar tana gina cibiyoyi guda uku a kowanne yanki na mazabar sanata a jihar domin horas da matasa a fannoni daban-daban, tare da basu takardar shaidar kwarewa.

Shima Daraktan Kamfanin Nigerian Breweries PLC, Mista Hans Essaadi, ya bayyana cewa cibiyar za ta koyar da matasa da mata sana’o’i kamar: Dinki Kera takalma Kitso da gyaran gashi Kere-keren na’urorin zamani (ICT) Ya ce za a tallafa musu da kayan fara sana’a da horo daga masu gogewa don tabbatar da sun zama ‘yan kasuwa masu cin gashin kansu.

A karshe, Mataimakiyar Gwamna ta jaddada kudirin gwamnatin jihar na kara karfafa yanayin zuba jari.

“Gwamnatin Gwamna Uba Sani ta kuduri aniyar samar da kyakkyawan yanayi ga masu saka jari domin a gina Kaduna mai cike da damammaki ga kowa,” ta jaddada.

Ta kuma gode wa Nigerian Breweries PLC bisa wannan gagarumar gudummawa, tana mai bayyana ta a matsayin shaida na cikakken kishin al’umma da ci gaba mai dorewa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.