Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamnatin Kaduna Za Ta Sake Ganawa da Membobin ASUU-KASU

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana shirinta na ganawa da membobin kungiyar ASUU na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) don warware batun yajin aikin da ke gudana.

Sakatare Din-din-din na Ma’aikatar Ilimi, Alhaji Rabiu Yunusa, ne ya bayana haka yayin ganawa da manema labarai a Kaduna.

In da yace gwamnati da shugabancin jami’ar jihar Kaduna KASU za su gana da mambobin ASUU-KASU domin cimma matsaya.

Tun farko an riga an samu fahimta kafin fara wanna yajin aiki, inda bashin da ake bi gwamnati ya kai kusan Naira biliyan 4, wanda Gwamna Uba Sani ya gada daga gwamnatin baya. ya kuma amince za a biya bashin a matakai. A cewar sa.

Alhaji Rabiu ya ja hankalin ASUU cewa yajin aiki da takeyi, zai iya lalata cigaban da KASU ta samu, ciki har da sahalewar Sabin darussa tara a tsangayar kimiyya da Gwamna Uba Sani ya taimaka da Naira miliyan 290 don samu.

Sanan akwai ginin tsangayar engineering, wanda ake kan ginawa a sabon jami’ar na din-din-din, wanda kamala tsangayar zai kara sa jami’ar jihar Kaduna KASU, ta zarce wa sauran jamio’in jihohi.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.