Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamnatin Kaduna za ta Ƙara Saka Jari a Fannin Illimi

Published

on

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr Hadiza Sabuwa Balarabe, ta ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa jami’o’inta domin su shiga sahun gaba a jerin manyan jami’o’in duniya.

Daraktan Hukumar Inganta Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna, Farfesa Usman Abubakar Zaria, ne ya wakilci mataimakiyar gwamnan a taron Rijistarori na Jami’o’in Najeriya (ARNU) karo na uku da aka gudanar a Jami’ar Jihar Kaduna.

Ya ce gwamnati na ɗaukar matakai na musamman wajen horas da ma’aikata da kuma samar da kayan aiki, domin ciyar da jami’o’in gaba da tabbatar da sahihiyar gudanarwa.

Taron, mai taken “Matsayin Jami’a a Gasar Duniya”, ya hada Rijistarori daga jami’o’i fiye da 50, inda suka tattauna hanyoyin inganta gudanarwar jami’o’i da kuma bunkasa bincike da darajar takardun shaida.

Kungiyar ARNU ta bukaci gwamnati da ta kara mayar da hankali kan manufofin da za su taimaka wa jami’o’in Najeriya su samu matsayi mai kyau a fannin ilimi na duniya.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.