Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Gwamnatin Kaduna da Jobberman Sun Kaddamar da Taron Ayyuka don Tallafa wa Matasan da Ke Neman Aiki

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna, tare da hadin gwiwa Jobberman da Mastercard Foundation, ta gudanar da sabon taron neman aiki karo na biyu a dakin taro na Umaru Musa Yar’adua dake dandalin Murtala a birnin Kaduna, domin taimaka wa matasa da damar samun aikin yi mai inganci.

“Kaduna Career Fair 2025”, na wanan shekara ya hada matasa sama da 1,000 da ke neman aiki, tare da kamfanoni fiye da 100 masu guraben aiki da za a cike nan take ko a cikin watanni masu zuwa.

Da take jawabi a wajen taron, Kwamishinar Ma’aikatar Kasuwanci, Kirkire-Kirkire da Fasaha, Hon. Patience Fakai, ta bayyana cewa gwamnatin Sanata Uba Sani na kokarin mayar da jihar Kaduna cibiyar horar da matasa a fannin kwarewa da fasaha a Najeriya.

Ta ce, “Mai girma Gwamna, Sanata Uba Sani, yana gina cibiyoyin koyon sana’o’i da fasahar zamani guda uku, guda daya a kowace mazabar sanata domin karfafa cigaban dan adam a jihar.”

Kwamishinar ta kara da cewa horar da matasa da samar musu da ayyuka zai taimaka wajen karfafa tattalin arziki, samar da arziki, rage zaman banza da talauci a cikin al’umma.

Taron karo na farko da aka gudanar a ranar 23 ga Nuwamba, 2023, ya samu halarta matasa 1,496 da ke neman aiki, tare da wakilai 71 daga kamfanoni, inda aka riga aka tabbatar da fiye da 300 sun samu aiki.

A wannan taron na bana, matasa biyar sun riga sun samu guraben aiki, kuma ana sa ran karin nasarori a cikin makonni masu zuwa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.