Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Illimi

Gwamnatin Jihar Kaduna Tayi Alkawarin Tallafa wa Sabuwar Jami’ar Tarayya Kachia

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya karɓi tawagar shugabancin sabon jami’ar Federal University of Applied Sciences, Kachia, ƙarƙashin jagorancin Babban Malami addinin kirista, Bishop Matthew Hassan Kukah.

A yayin ziyarar, Bishop Kukah ya yaba da namijin ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. Ya bayyana cewa jami’ar ta kammala shirin fara shirin karatu guda 18 a watan Satumba 2025.

Bishop Kukah ya roƙi gwamnatin jihar da ta ƙara kaso na fili, gina titin shiga jami’ar, samar da motoci da kuma ƙarfafa tsaro a yankin jami’ar. Ya kuma tabbatar da goyon bayan cikakke ga gwamnatin jihar domin ganin jami’ar ta zama cibiyar ilimi mai daraja a duniya.

A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya gode wa tawagar bisa ziyarar da kuma rawar da Bishop Kukah ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya. Ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki ba a sake samun rikicin addini ko kabilanci a jihar ba.

Gwamnan ya sanar da cewa TETFUND za ta tallafa wa jami’ar, tare da ƙarin fili daga gwamnatin jihar. An kuma umurci hukumar KADRA ta gaggauta gyaran hanyar shiga jami’ar. Motoci za a samar, kuma ana haɗa kai da Hedikwatar Tsaro don ƙarfafa tsaro a yankin Kachia.

Gwamna Uba Sani ya miƙa godiya ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da sauran manyan jami’an gwamnati bisa tallafin da suka bayar don ganin an kafa wannan jami’a mai tasiri.

Federal University of Applied Sciences, Kachia za ta zama tushen ci gaban tattalin arziki, kirkire-kirkire da haɓaka ilimi a Kaduna da Najeriya gaba ɗaya.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.