Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kaddamar da Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya Don Tabbatar da Dorewar Tsaro a Fadin Jihar

Published

on

A kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na tabbatar da zaman lafiya, inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta kaddamar da Kwamitin Dabarun Tsaro da Zaman Lafiya (PSPSST).

An gudanar da taron kaddamarwar ne a fadar gwamnati jihar Kaduna, inda mataimakiyar gwamnan ta jagoranci zaman farko na kwamitin da ta bayyana a matsayin mai matukar muhimmanci ga makomar jihar.

“Wannan aiki ba karamin nauyi ba ne,” in ji Dr. Balarabe. “Amma na yi imanin cewa wannan kwamiti zai iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, bisa kwarewa, hangen nesa da jajircewar da muke da shi.”

Ta jaddada cewa matsalolin tsaro a jihar suna bukatar hadin kai daga dukkan bangarori — daga gwamnati zuwa al’umma. Ta ce: “Tsaro ba aikin gwamnati kadai ba ne. Hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati da jama’a. Dukkanmu muna da rawar da za mu taka.”

A cewarta, kwamitin zai fara da nazarin hadurran tsaro da suka addabi yankuna daban-daban, da duba yadda ake gudanar da ayyuka yanzu, sannan su tsara sabbin dabaru masu amfani. Ta kara da cewa, “Ba wai kawai za mu rubuta rahotanni ba ne. Muna son daukar matakan da za su kawo canji na gaskiya ga rayuwar mutane.”

Kwamitin na da wakilai daga ma’aikatun gwamnati daban-daban da hukumomin tsaro, tare da goyon bayan ma’aikatar harkokin tsaro na cikin gida da sauran abokan hulda.

A karshe, Dr. Balarabe ta bukaci dukkan mambobin kwamitin da su kawo hazaka, shawarwari da himma a tafiyar da ke gaban su.

“Zaman lafiya zai yiwu. Amma yana bukatar jajircewa da hadin kai,” inji ta.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.