Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Lafiya

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kaddamar da Kwamitin Tsare-tsare Don Magance Zazzabin Cizon Sauro

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da kwamitin tsare-tsare na musamman domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta hanyar amfani da tsarin Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) da kuma Azithromycin Mass Administration (AZM).

Kwamishinar Lafiya ta jihar, Hajiya Umma K. Ahmed, ce ta jagoranci bikin kaddamar da kwamitin, inda ta jaddada cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, na da cikakken goyon baya wajen ganin an kawar da zazzabin cizon sauro daga jihar gaba ɗaya.

A cewar Kwamishinar: “Gwamnatin jihar tana aiki tare da abokan ci gaba wajen samar da kayan aiki da kuma fasaha don inganta fannin kiwon lafiya a jihar.”

Dr. Aishatu Abubakar Sadiq, Babbar Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, za ta shugabanci kwamitin. Kwamitin na da alhakin tsara yadda za a aiwatar da rarraba maganin AZM da kuma tsarin SMC a dukkan kananan hukumomin jihar. Haka zalika, kwamitin zai rika tara kayan aiki da kudi domin nasarar shirin.

Masu ruwa da tsaki da suka halarci bikin sun hada da: Dr. Sadiq Abubakar Idris, Daraktan Lafiyar Jama’a, Alhaji Hamza Ikara, Daraktan Kula da Cututtuka, Pharm. Isa Abubakar Balarabe, Daraktan Ayyukan Magunguna, Manajoji daga shirin kawar da cututtukan (NTDs), Wakilan shirin kawar da zazzabin cizon sauro na jihar, Wakilan Malaria Consortium da sauran kungiyoyi masu goyon baya.

Wannan mataki wata alama ce ta dagewar gwamnatin jihar wajen samar da lafiyayyun al’umma tare da rage yawan mace-macen yara da mata masu juna biyu da cutar zazzabin cizon sauro ke haddasawa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.