Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Dakta Uba Sani, ya isa garin Jere da ke karamar hukumar Kagarko domin wakiltar Shugaban Ƙasa, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, a wajen bikin kaddamar da aikin sake gina babban titin Abuja-Kaduna-Kano.
Titin da ake magana akai na daga cikin manyan hanyoyin da ke da matuƙar muhimmanci ga harkokin sufuri da kasuwanci a arewacin Najeriya, kuma aikin sake gina shi zai kawo sauƙi ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke amfani da hanyar kowace rana.
A wajen taron, an samu halartar manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa masu tasiri a ƙasa, ciki har da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi; Ministan Jiha na Ayyuka, Alhaji Bello Muhammed Goronyo; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero; Sanata Danjuma Laah; da Sanata Suleiman Usman Hunkuyi.