Gwamna Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya Taya tsohon gwamna jahar Kaduna Malam Nasiru Elrufai murna cika Shekara 65 a duniya.
A wani sokon taya murana da gwamna ya walafa a shafin sa na facebook, Uba Sani ya ce” Ina mika gaisuwa ta musamman da fatan alheri ga dan’uwana, abokina, tsohon gwamna, Mai Girma Malam Nasir El-Rufai CON, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 65. Ina rokon Allah Mai Girma ya ci gaba da maka jagoranta, kariya da kuma ƙarfafa ka.”