Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Da Dumi Dumin Sa

Gwamna Uba Sani Ya Naɗa Sarkin Kauru a Matsayin Amirul Hajj na Jihar Kaduna

Published

on

Mataimakiyar Gwamna Kaduna tare da Sarkin Kauru.

Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata (Dr) Uba Sani, ya naɗa Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar gwamnatin jiha domin aikin Hajjin 2025.

A sanarwar da sakataren yaɗa labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya fitar a yau 24 ga maris, 2025, ya bayyana cewa an naɗa Sarkin Kauru ne bisa ƙwarewarsa, kyakkyawan shugabancinsa, da kuma kwarewarsa wajen tafiyar da al’amuran jama’a.

A matsayinsa na amirul hajj, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman zai jagoranci shirin aikin hajjin jihar Kaduna, tare da aiki kafada da kafada da kwamitin hajj na Musamman na jihar, da sauran hukumomin da abin ya shafa a matakin jiha, tarayya da na ƙasa da ƙasa. Ana sa ran zai jagoranci shirye-shirye da aiwatar da dukkan matakai don tabbatar da cewa maniyyatan jihar Kaduna sun sami damar gudanar da aikin Hajji cikin nasara, tsari da sauƙi.

Da yake taya sabon amirul hajj murna, gwamna Uba Sani ya jaddada amincewarsa da ƙwarewarsa, tare da yin kira gare shi da ya yi amfani da ilimi da basirarsa wajen gudanar da wannan nauyi. Gwamnan ya kuma yi masa fatan samun nasara tare da jagorancin Allah a wannan sabuwar aiki da aka ɗora masa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.