Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamna Uba Sani ya nada sabbin kwamishinoni, ya kirkiri sabuwar Ma’aikatar Yada Labarai a Kaduna

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nada sabbin kwamishinoni guda biyu tare da canja wurin aiki ga wani tsohon kwamishina, a wani mataki da gwamnatin ke cewa zai taimaka wajen inganta shugabanci da gudanarwa a fadin jihar.

A cikin sabbin nadin, Farfesa Abubakar Sani Sambo ya zama sabon kwamishinan Ilimi na jihar. Haka zalika, Gwamna Uba Sani ya kirkiri sabuwar Ma’aikatar Yada Labarai tare da tura tsohon kwamishinan ilimi, Farfesa Sani Bello (Mainan Zazzau), ya jagoranci ta.

Kazalika, Barrister Gloria Ibrahim ta samu mukamin kwamishinar harkokin matasa.

Farfesa Sambo, wanda ya shahara a fannin makamashi, ya rike mukaman mataimakin shugaban jami’a da shugaban jami’a a wasu manyan cibiyoyin karatu a Najeriya, ciki har da ATBU Bauchi da KASU. Ya kuma jagoranci Hukumar Makamashi ta Kasa daga 2005 zuwa 2012, sannan ya zama mai ba shugaban kasa shawara kan makamashi a 2011.

Barrister Gloria kuwa kwararriya ce a fannin lauya da sasanci. Ta shugabanci kamfanin Glownom Legal Consult a Kaduna, kuma memba ce a kungiyoyin NBA da FIDA da sauran ƙungiyoyin masu kare hakkin yara da matasa.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa yana sa ran sabbin kwamishinonin za su kawo sabbin dabaru wajen aiwatar da manufofin gwamnati, musamman a fannin ilimi da ci gaban matasa.

Nadin ya fara aiki ne nan take.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.