Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da nadin sabbin manyan jami’ai domin karfafa ayyukan gwamnati da bunkasa ingancin shugabanci a ma’aikatun gwamnati.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ibraheem Musa, Sakataren Yada Labarai na Gwamna, ya fitar a yau 17 ga Afrilu, 2025.
Wadanda aka nada sune:
Jummai Bako – Shugabar Ma’aikata ta Jihar Kaduna.
Ibrahim Balarabe – Sakatare Janar, Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna.
CP Ali D. Audu (Rtd.) – Kwamandan Rundunar KADVIS (Kaduna Vigilance Service).
Gwamna Uba Sani ya bukaci sabbin shugabannin da su kasance masu gaskiya, jajircewa, da sadaukarwa, tare da amfani da kwarewarsu wajen kawo sauyi mai amfani.
Takaitacen Bayani Kan Sabbin Shugabanni:
Jummai Bako – Tana da MBA daga KASU da digiri a Tattalin Arziki daga BUK. Tsohuwar Babbar Sakatare ce, kuma ta rike mukamai masu yawa a ma’aikatun gwamnati. Tana da kwarewa a kasafi, tsare-tsare, da hulda da jama’a.
Ibrahim Balarabe – Ya yi aiki na fiye da shekaru 30 a fannin kudi da fansho, ciki har da matsayi na Darakta a Access Pensions. Ya samu digirinsa daga ABU Zaria.
CP Ali D. Audu (Rtd.) – Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda a Kaduna, kuma kwararre ne a fannin tsaro da horarwa. Ya rike mukamai a matakin kasa da kasa a rundunar ‘yan sanda.
Gwamnan ya taya su murna tare da fatan nasara a sabbin mukamansu.