Connect with us

Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Mayar da Takardun Mallakar Filayen Fifth Chukker

Published

on

A kuduri aniyar ƙirƙirar yanayin kasuwanci mai kyau wanda zai karfafa zuba jari da habaka tattalin arziki a jihar Kaduna, domin samar da ayyukan yi da kuma inganta kudaden shiga na cikin gida gwamna Uba Sani ya mayar da filaye 4 ga Fifth Chukker wanda tsohon gwamnati ta soke.

Daraktan hukumar filaye ta Kaduna (KADGIS), Dr. Bashir Ibrahim Garba, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, a Kaduna.

Dr. Garba ya bayyana cewa Gwamnan ya mayar da takardun mallakar filaye hudu na Fifth Chukker Resort Limited, wadanda gwamnatin baya ta soke, yana nuna jajircewarsa wajen ƙarfafa yanayin kasuwanci a Jihar Kaduna.

Fifth Chukker Polo da Country Club yana kan hanyar Jos, tare da kyakkyawan muhalli mai yalwa, wanda ke daukar bakuncin wasannin polo da manyan gasar kasa da kasa da ke jan hankalin masu kallo daga sassa daban-daban na duniya.

Daraktan Hukumar ya kuma bayyana kudirin gwamnati na magance takaddamar mallakar filaye da kadarori, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin ƙasa mai inganci da zai amfanar da al’umma.

Dr. Garba ya nuna kwarin gwiwa cewa dawo da wadannan filaye zai taimaka wajen warware matsalolin soke mallakar filaye da aka yi a baya ba tare da bin ka’ida ba.

Ya jaddada cewa warware wadannan matsaloli zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki, wanda hakan zai hanzarta ci gaban tattalin arziki a Jihar Kaduna.

Daraktan ya kuma yi kira ga al’ummar Kaduna da su kasance masu bin doka da oda tare da yin hakuri yayin da gwamnati ke aiwatar da gyare-gyaren dokokin filaye da suka dace da bukatun jama’a.

Copyright © 2024 kaduna Reports.