Connect with us

Siyasa

Gwamna Uba Sani Ya Karba Bakwancin Minister Jinkai

Published

on

Gwamna jahar Kaduna Sen. Uba Sani ya karbi bakwancin minister jinkai Prof. Nentawe G. Yilwatda a gidan gwamnati na Sir Kashim dake birnin jihar Kaduna.

Bayani hakan na kunshe a wani rubutun da gwamna ya walafa a shafin sa na facebook, a ranar talata.

Cikin abubuwa da suka maida hankali gun tattaunawa a yayin ziyarar, shine kan batun qananan yaran da aka sako daga hanun jami’an tsaro yan sanda bisa umarni shugaban kasa Nijeria Ahmad Bola Tinubu (GCFR), tare da batutuwan guraren dake bukatan talafin da sauransu.

A yayin jawabin sa, ministan ya yaba ma gwamnati jihar Kaduna akan matakin da ta dauka na kawo karshen matsala tsaro a jihar tare kudirin gwamnati na kawar da talauchi, wanda yace yayi daidai da shirin shugaban kasa na renew hope agenda a turance.Hakan kuma ya kara da yabon salon gudanar da gwamnati jihar Kaduna wanda ya alakanta shi da samun karuwa masu dawowa jam’iyar APC daga manyan jami’un adawa a fadin jahar.

Gwamna Uba Sani ya sheda ma ministan cewa, suna kan shirye shirye koya ma qananan yaran sana’oi a cibiyoyin koyar da sana’a don yaran su afanar da kansu da kasa baki daya.

Gwamna yayi godiya da kira kan kawance tsakanin gwamnati jihar Kaduna da kuma ministirin jinkai tare da gode ma shugaban kasa na gudumawar da yake ba ma gwamnati Kaduna.

Copyright © 2024 kaduna Reports.