A yau, Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Senator Uba Sani, tare da goyon bayan Majalisar Karamar Hukumar Kagarko, ya kaddamar da aikin sake haɗa wutar lantarki a karamar hukumar. Wannan aikin zai magance matsalar wutar lantarki a yankin kuma ya inganta rayuwar al’umma.
Taron kaddamarwar ya samu halartar Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Muhuyideen A. Umar, wanda ya bayyana muhimmancin aikin. Haka kuma, an samu halartar Mai Ba Gwamna Shawara kan Ci gaban Karkara, wakilin Ministan Harkokin Kananan Hukumomi, Darakta Janar na Kamfanin Wutar Lantarki na Kaduna (KAPSCO), da sauran shugabannin gargajiya, addini, da jiga-jigan APC a Kagarko.
A cikin jawabin sa, Hon. Muhuyideen A. Umar ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa kokarin da ya yi wajen magance matsalar wutar lantarki.
Ya bayyana cewa “wannan aikin zai inganta rayuwar mutanen Kagarko, ya kara habaka ci gaban tattalin arziki, da kuma kara inganta tsaro a yankin.”
Aikin na sake haɗa wutar lantarki zai kawo ci gaba mai ma’ana ga Kagarko, inda za a samu ingantacciyar wutar lantarki wanda zai taimaka wajen habaka kasuwanci da rage wahalar rayuwa a yankin.