Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ta bakin Kwamishinan Shari’a na jihar, Sule Shuaibu (SAN), ya jinjinawa Hukumar DSS bisa cafke ‘yan bindiga da masu safarar makamai guda 54 a jihar.
Hukumar ta gudanar da ayyuka 34 da suka kai ga kama bata-gari daban-daban, ciki har da masu ba da bayanan sirri, masu safarar makamai, da masu satar mutane.
An kwato bindigogi da dama, ciki har da AK-47 guda biyar, GPMG guda daya, RPG guda uku, da harsasai sama da 5,000. Haka kuma, an ceto mutane 79 da aka sace.
Daga cikin wadanda aka kama akwai jami’in tsaro da aka samu da laifin satar harsasai 217 domin sayarwa ‘yan bindiga, da wani mai safarar harsasai 500 zuwa Birnin Gwari.
Gwamna Sani ya gode wa DSS karkashin jagorancin Mr. Oluwatosin Ajayi, tare da bukatar hadin kan al’umma domin dorewar zaman lafiya.