Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna godiya ga Alhaji Aliko Dangote bisa agajin buhunan shinkafa 35,000 domin rabawa a dukan kananan hukumomi 23 na jihar.
Shirin, wanda Gidauniyar Dangote ta dauki nauyi, na daga cikin kokarin yaki da yunwa da talauci a Najeriya, karkashin Dangote National Food Intervention Project.
A jawabinsa da Shugaban Ma’aikatansa, Alhaji Sani Liman Kila, ya karanta, Gwamna Uba ya ce, “Wannan tallafi na nuna kulawa da tausayi, kuma yana goyon bayan manufofin gwamnatinmu na taimaka wa masu karamin karfi.”
Wakilin Gidauniyar Dangote, Alhaji Sadiq Ahmed, ya ce tallafin zai amfani fiye da mutane miliyan daya a Najeriya, kuma ya shafi dukkan kananan hukumomi 774.
“Tallafin yana nuni da yadda Gidauniyar ke daukar nauyin jin dadin al’umma a matsayin ginshikin ci gaba,” in ji shi.