Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Illimi

Gwamna Uba Sani Ya Biya Bashin Kuɗin Makarantun Ɗalibai Dake Karatu a Ƙasashen Waje

Published

on

Gwamna Uba Sani ya biya bashin kuɗin makaranta na ɗaliban Jihar Kaduna da ke karatu a ƙasashen waje, wanda ya kai $247,235.84 (Naira miliyan 407,937,750). Wannan biyan kuɗin ya shafi ɗaliban da suka yi karatu a fannonin Likitanci da Nursing, waɗanda aka bar su cikin matsala daga gwamnatin da ta gabata.

Jami’o’in Da Aka Biya Sun Hada Da:

Debrecen University (UK/Hungary): An biya $51,400 (Naira miliyan 84,810,000)

University of Wollongong (Dubai): An biya $13,827.08 (Naira miliyan 22,814,550)

Havana Medical University (Cuba): An biya $164,010 (Naira miliyan 270,616,500)

KIU IUIU (Uganda): An biya $17,998 (Naira miliyan 29,696,700)

Farfesa Yahya Saleh Ibrahim, Shugaban Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kaduna, ya bayyana cewa wannan mataki na Gwamna Uba Sani yana da nufin taimaka wa ɗalibai da suka yi rashin damar kammala karatunsu ko sabunta biza.

A cewar Farfesa Ibrahim, Gwamna Uba Sani ya kuma biya kuɗin makaranta na ɗaliban daga shekarar 2023 zuwa yanzu. Gwamnan ya umarci Hukumar Tallafin Karatu ta duba matsayin biyan kuɗi a sauran jami’o’in da ɗalibai daga Jihar Kaduna ke karatu domin tabbatar da cewa babu wani bashi da aka bar baya.

Wannan mataki yana ƙara tabbatar da jajircewar Gwamna Uba Sani wajen tallafa wa ɗalibai, musamman na talakawa, da kuma ci gaban ilimi a jihar.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.