Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Sabbin Matakai Don Inganta Noma a Taron Kaddamar da NAPM a Abuja

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci taron kaddamar da tsarin National Agribusiness Policy Mechanism (NAPM) a fadar shugaban kasa, Abuja.

An shirya taron ne don hada kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen bunkasa noma da kasuwanci.

A jawabinsa, Gwamnan ya ce noma na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa, yana mai cewa:

“Muna sauya noma daga aikin gargajiya zuwa tsarin zamani da ya dogara da kasuwa.”

Ya bayyana cewa Kaduna tana kan gaba da manufofi kamar Contract Farming Policy, Soybean Policy, da Gender in Agriculture Policy, domin karfafa manoma da jawo masu zuba jari.

Gwamnan ya gode wa gwamnatin tarayya da abokan hulda irin su AGRA, World Bank, da Ma’aikatar Noma ta Tarayya, bisa hadin kai wajen ciyar da fannin noma gaba.

“Tare zamu gina tsarin noma mai dorewa da zai yaki yunwa, talauci da rashin aikin yi,” in ji Gwamnan.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.