Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Gwamna Uba Sani da Kakakin Majalisar Wakilai Sun Gwangwaje Sarakunan Gargajiya da Motoci

Published

on

A wani gagarumin mataki na goyon baya ga masarautun gargajiya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani tare da Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, sun mika sabbin motoci guda 23 ga sarakunan gargajiya 19 da ke fadin jihar.

An gudanar da bikin mika motocin ne a fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, Sir Kashim Ibrahim House, inda sarakuna na farko da na biyu suka karɓi motocin domin inganta ayyukansu na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankunansu.

Gwamna Uba Sani, tare da mataimakiyarsa, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, suka jagoranci wannan biki da ya samu halartar ‘yan majalisun tarayya da na jiha, manyan jami’an gwamnati da kuma baki masu daraja.

Motocin dai hukumar SMEDAN ce ta bayar da su, bisa kokarin da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi domin tallafawa sarakunan wajen sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

Wannan shiri yana nuna kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da majalisar tarayya, inda ake aiki tare don ci gaban al’umma.

A jawabinsa, Sarkin Zazzau kuma shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, Mai Martaba Ambasada Nuhu Bamalli, ya bayyana godiya ta musamman ga gwamnatin jihar da Kakakin Majalisar, yana mai cewa motocin za su taimaka matuka wajen isa ga al’ummomi da kuma magance matsaloli cikin gaggawa.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.