Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Dan Takarar Majalisar Wakilai na Chikun/Kajuru, Comrade Yakubu Waziri, Ya Gyara Titin Maraban Rido, Ya Bukaci Al’umma Su Goyi Bayan Gwamna Uba Sani

Published

on

Hoto: FB/Kaduna political Affairs

Maraban Rido, Kaduna – Wani ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Chikun/Kajuru, Comrade Yakubu Waziri, ya gudanar da aikin gyaran titin Maraban Rido, wata muhimmiyar hanya da ke amfani da al’ummar yankin.

A kokarinsa na inganta ababen more rayuwa, Comrade Waziri ya bayyana cewa wannan aiki yana daga cikin shirin da ya ƙaddamar don tallafa wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wajen kawo ci gaba ga al’umma.

Yayin jawabin da ya yi wa mazauna yankin, Waziri ya bukace su da su mara wa gwamnatin Gwamna Uba Sani baya, domin ci gaba da jin daɗin romon dimokuraɗiyya.

“Muna bukatar hadin kai da goyon bayan ku domin ci gaba da ayyukan ci gaba. Lokacin zaɓe idan ya zo, ku zaɓi APC daga sama har ƙasa,” in ji Waziri.

Ya kuma bayyana cewa babbar manufarsa ita ce rage wahalar da talakawa ke fuskanta, musamman a bangaren sufuri, domin duk wani ci gaba yana da nasaba da kyawawan hanyoyi.

Hoto: FB/Kaduna Political Affairs

Bukatar Transformers: Waziri Ya Yi Alkawari

A yayin taron, wasu mazauna yankin sun bukaci karin na’urorin wutar lantarki (transformers) don magance matsalar wuta a yankin. Da yake mayar da martani, Waziri ya tabbatar da cewa ya saurari kokensu, kuma zai dauki matakin da ya dace.

“Mun ji buƙatar ku kan transformers. Muna tafiya a hankali, mataki bayan mataki. Da yardar Allah, za mu kai ga hakan,” in ji shi.

Shugaban Yankin da Al’ummar Maraban Rido Sun Yaba

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Maraban Rido, Malam Auta Alkali, ya jinjinawa Comrade Waziri bisa wannan kokari.

“Ina mika godiya ta a madadin al’ummar yankin ga ɗan takararmu, Comrade Waziri. Idan mutum ya yi alƙawari kuma ya fara cika shi tun kafin ya hau mulki, babu dalilin da zai sa a yi shakkarsa. Muna addu’ar Allah Ya ba ka nasara,” in ji Sarkin.

Har ila yau, wani direban acaba, Solomon Iliya, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da wani dan siyasa ya kawo irin wannan aiki a yankin.

“Tun da dadewa, mu ‘yan acaba ne muke hada kai mu gyara hanyar, amma yau, Comrade Waziri ya kawo mana sauki. Muna godiya, kuma idan lokacin zaɓe ya zo, tabbas za mu rama wannan alheri,” in ji shi.

A halin yanzu, wannan aikin na daga cikin jerin ayyukan da Comrade Waziri ke aiwatarwa a mazabarsa domin kyautata rayuwar al’umma, yayin da ake tunkarar zaɓe mai zuwa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.