Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana burinsa na ganin Kaduna ta zama gidan zaman lafiya da kowa zai zauna ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci wani taro mai muhimmanci na Kwamitin Tsaro na Jihar Kaduna, wanda aka gudanar a ranar 29 ga Afrilu, 2025.
Gwamna Uba Sani Ya Ce: “Zamuyi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Jihar Kaduna ta zama “oasis of peace”. Wannan shi ne burina, kuma da hadin gwiwar jami’an tsaro da al’umma, za mu cimma hakan.”
Wasu Daga Cikin Nasarorin Tsaro da Aka Fadi a Taron Sun Hada Da:
Raguwar garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga a sassa daban-daban na jihar.
Farmakar maboyar ‘yan ta’adda da kuma kwato makamai da kama barayin kayayyakin gwamnati.
Habakar noma a shekarar da ta gabata saboda manoma sun samu damar noma cikin kwanciyar hankali.
Karuwar kudaden shiga daga Kaduna Inland Dry Port sakamakon zaman lafiya.
Gwamnan ya yaba da jajircewar hukumomin tsaro, musamman a wuraren da suka shahara da rikice-rikice kamar Birnin Gwari da Giwa, inda yanzu aka fara samun dawowar rayuwa da bunkasar kasuwanci.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa rundunonin tsaro don tabbatar da dorewar zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.