A cikin yanayin bukukuwan Ista, matasa 70 daga ƙungiyar LightWk sun gudanar da wani babban aikin duba lafiya kyauta a unguwar Hayin Banki da ke karamar hukumar Kaduna North, inda Musulmai da Kiristoci suka amfana tare.
Aikin, wanda aka gudanar a harabar cocin First Baptist , Hayin Banki, ya taimaka wa sama da mutane 250 cikin awa shida.
Wannan aiki ya zamo wani babban alamar zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban. Kodayake an fara tsara gudanar da aikin a wata makarantar gwamnati, sai aka sauya zuwa cocin sabida wani tasgaro da aka samu.
Sai dai hakan bai hana Musulmi fitowa da yawa ba, inda aka tarbe su cikin girmamawa da ƙauna daga abokan zamansu Kiristoci.
“Wannan rana ta tuna mana da yadda rayuwa take da sauƙi da ƙayatarwa idan muna zaman lafiya. Mun rungume juna, mun dariya, mun yi addu’a tare,” in ji Jeremiah, ɗaya daga cikin masu shirya aikin.
Aikin duba lafiyar ya kunshi gwaje-gwaje, bayar da magunguna, da shawarwarin likita dukkansu kyauta. Daga cikin wadanda suka bayar da gudummawa akwai likitoci, nas-nas, da masu aikin sa-kai daga ɓangarorin addinai daban-daban.
Wannan aiki na LightWk ya sake jaddada cewa zaman lafiya da hadin kai suna da yuwuwa a Najeriya, musamman idan al’umma za su ci gaba da girmama juna, kuma su hada hannu wajen cigaba.