Labarai

Bello Elrufai ya biya ma dalibai 130 kudin jarabawar JAMB

Published

on

Dan majalisa tarayya mai wakiltar al’umar kaduna ta Arewa Hon. Bello Elrufai, ya biya wa dalibai 130 kudin jarabawar JAMB na shekarar 2025/2026.

Bayanin hakan na kunshen ne a wata sanarwa da dan majalisar ya walafa a shafin sa na dandalin Facebook a ranar talata.

Dalibai 130 sun hada da dalibai daga unguwannin Ebira, kristoci da dalibai masu bukata ta musamandake gundumar Kaduna ta Arewa inda yake wakilta.

Bello ya kuma yabba da na mijin kokarin da kwamitin karkashin jagoranci mai bashi shawara akan harka illimi sukayi gun tabatar da aikin zakulo da biyan kudin ga dalibai.

Copyright © 2024 kaduna Reports.