Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana yadda tashin hankalin matsalar ruwan sha da jihar ke fama da ita ya shafi rayuwarsa tun bayan da ya hau mulki – har ma ya hana shi barci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyar daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a jihar, Sheikh Musa Assadus-Sunnah, a masallacinsa da ke Kaduna.
Yayin ziyarar, Sheikh Musa Assadus-Sunnah ya gabatar da koke-koken al’umma, inda ya bukaci Gwamna Uba Sani da ya maida hankali kan matsalar ruwan sha da ke addabar al’ummar jihar a lungu da sako, yana mai cewa lamarin yana da matukar tayar da hankali.
A martaninsa, Gwamna Uba Sani ya ce: “Ni kaina tun da na hau mulki na fuskanci matsalar ruwan sha da jihar ke fama da ita. Hankalina ya tashi matuka – har bana iya barci.”
Ya kara da cewa, a lokacin da ya hau mulki, kaso 6 cikin 100 ne kawai na ruwan sha ake iya samarwa ta hannun hukumar kula da ruwa a jihar. Amma a halin yanzu, an samu ci gaba – inda ake samun kaso 30 cikin 100 na ruwan sha.
Gwamna ya tabatar da cewa matsala ruwan zata zo karshe daganan zuwa watan disamba, domin gwamnati sa ta dau matakai da suka adabe matsala ruwan sha a jihar.