Connect with us

Siyasa

Ba Don Mukami Ko Takara Yasa Na Dawo APC ba – Mukhtar Ramalan Yero

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa matakin nasa ya samo asali ne daga burinsa na ba da gudunmawa ga ci gaban jihar.

Yero ya jaddada cewa sauya shekarsa ba don burin siyasa ko neman wani mukami ba ne, sai dai domin sadaukar da kansa wajen mara wa gwamnatin Uba Sani baya.

“Ina so in bayyana a fili cewa shawarar da muka yanke na komawa APC ba don neman wata kujera ta siyasa ko mukami ba ne. Wannan shawara ce ta kashin kaina domin ba da gudunmawata ga ci gaban jiharmu a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna na yanzu, Sanata Uba Sani,” in ji shi.

Copyright © 2024 kaduna Reports.