Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

ASUU KASU Ta Koma Yajin Aiki: Dalilai 7 Da Suka Haifar Da Rikici

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta sanar da komawa yajin aikin da aka dakatar, wanda zai fara nan take daga yau, Laraba 24 ga watan Afirulu, 2025.

Sanarwar da ta fito daga kwamitin sanarwa kungiyar mai dauke da sa hanun shugaban reshen ASUU-KASU, Dr. Peter Adamu, da sakataren kungiyar, Dr. Peter Waziri.

In za’a tuna a ranar 18 GA watan faburairu 2025, kungiyar ASUU-KASU ta tsunduma yajin aiki, in da bisani tajenye yajin aikin ranar 22 ga watan, biyo bayan cima yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnati jihar Kaduna.

ASUU-KASU ta tabbatar da cewa kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ya amince da komawar yajin aikin sai mama ta gani.

Me ya haifar da yajin aikin ASUU-KASU 2025?

Ga manyan matsalolin da ASUU-KASU ke kuka da su:

  1. Rashin biyan albashi daga Mayu zuwa Satumba 2022 da wasu watanni.
  2. Biyan hakkokin malaman jami’a (EAA) tun daga 2016.
  3. Biyan bashin karin girma da SIWES.
  4. Haqqin malaman da suka rasu – ciki har da Group Life Assurance.
  5. Rashin biyan fansho daga 2009 zuwa 2019.
  6. Gaza aiwatar da karin albashi na kaso 25% da 35%.
  7. Kiran ASUU da a dawo da ‘yancin jami’o’i.

Copyright © 2024 kaduna Reports.