Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP, Hon. Isa Mohammed Ashiru, ya zargi gwamnatin jihar karkashin APC da gaza kula da makomar ilimi, yana mai cewa yajin aikin ASUU-KASU ya bayyana gazawar gwamnati.
A wata sanarwa da ya fitar, Ashiru ya bayyana yajin aikin da malaman jami’ar jihar Kaduna (KASU) suka fara a matsayin abin kunya da alama ta gazawar gwamnati wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Malaman Jami’ar Jihar Kaduna sun fara yajin aiki yau bisa zargin saba yarjejeniya da kin biyan hakkokinsu.
Ashiru ya bayyana hakan a matsayin abin kunya da ke nuni da yadda gwamnati ke tauye hakkin malamai da dalibai.
“Yajin aikin nan ba rikicin albashi kawai ba ne. Hujja ce ta tauye haqi da gwamnatin APC ke yi wa ilimi, tare da durkusar da makomar matasa.” in ji Ashiru.
Ya ce bukatun ASUU na da tushe a doka da tsarin mulki, kuma gwamnatin ba ta da wata hujja da za ta hana biyan hakkokin malamai.
Ashiru ya bukaci a kawo karshen yajin aikin nan take, tare da sake fasalin tsarin kula da harkokin ilimi a jihar.