Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

ASUU-KASU Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba Gwamnati Wata Dama Har Zuwa 30 ga Watan Yuni

Published

on

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU reshen Jami’ar Kaduna (KASU) ta dakatar da yajin aikin da ta fara tun ranar 24 ga Afrilu, 2025.

A wata takarda da ta aikewa shugaban jami’ar, kungiyar ta ce dakatarwar na nan take daga ranar Alhamis, 16 ga Mayu, 2025.

Takardar ta nuna cewa uwar kungiyar ASUU a matakin ƙasa ce ta amince da bukatar ASUU KASU na dakatar da yajin aikin domin ba gwamnati damar cika yarjejeniyar da suka cimma.

Kungiyar ta ce za su sake komawa taro ranar 30 ga Yuni, 2025 don duba matakin da gwamnati ta dauka kan aiwatar da yarjejeniyar.

ASUU KASU ta ce dakatar da yajin aikin ba yana nufin an magance matsalolin ba, sai dai suna ba gwamnati lokaci don ta gyara.

Rahoton ya kunshi sa hannun shugaban ASUU KASU na rikon kwarya, Dr. Abubakar Abdullahi da sakatare, Dr. Peter M. Waziri.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.