Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Siyasa

APC Arewa maso Yamma ta Amince da Tinubu a Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na 2027

Published

on


Shugabannin jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaben 2027.

An yanke wannan shawara ne a taron masu ruwa da tsaki na APC na yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda shi ne mai kula da jam’iyyar a shiyyar.

Taron ya samu halartar Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Kakakin Majalisar Wakilai Rt. Hon. Tajudeen Abbas, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnonin Kebbi da Jigawa, Mataimakin Gwamnan Katsina, ministoci daga Arewa maso Yamma, ‘yan majalisun dokoki, da shugabannin jam’iyya daga jihohin shiyyar.

Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya gabatar da kudurin goyon bayan Tinubu, wanda Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya mara wa baya. Daga nan Kakakin Majalisar ya sanya kudurin a kuri’a, inda mahalarta taron suka amince da murya ɗaya.

A bayan taron, Sanata Uba Sani ya karanta sanarwar da ta ƙunshi godiya ga Shugaba Tinubu bisa wakilci da ayyuka da ya bai wa yankin, ciki har da ministoci 12, shugabannin tsaro biyu, da ci gaban ayyukan ababen more rayuwa.

Sanarwar ta ce tsaro ya inganta a yankin, lamarin da ya ba manoma damar komawa gonaki. Haka kuma ta ce APC tana samun karɓuwa a yankin bisa nasarorin da shugabanni ke samu.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.