Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

An Nada Matar Sanata Katung, Abigail Marshall Katung Sarautar Gimbiyar Jaba

Published

on

A wani babban biki na al’ada da tarihi, Abigail Marshall Katung, matar Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Barr. Sunday Marshall Katung, ta samu karramawar sarautar Gimbiyan Jaba (Princess of Ham) daga Mai Martaba Kpop Ham, Dr. Danladi Gyet Maude, OON.

An gudanar da nadin sarautar ne a garin Kwoi na jahar Kaduna, cibiyar al’ummar Ham, inda manyan baki daga sassa daban-daban suka halarta domin taya murna da nuna goyon baya.

Sauran fitattun ’ya’yan Ham da aka nada sarauta sun haɗa da:

Janar Martin Luther Agwai – Sarkin Yakin Jaba (Ham), Barr. Dr. Deborah Usman – Jakadiyan Jaba (Ham), Dr. Gideon Jock – Hasken Jaba (Ham) da kuma Dr. Dogara Gyet – Jagaban Jaba (Ham).

Sanata Sunday Marshall Katung ya bayyana wannan karramawa a matsayin hujjar irin gudummawar da matarsa da sauran waɗanda aka karrama ke bayarwa ga ci gaban ƙasar Ham da al’ummar Najeriya baki ɗaya.

“A madadin mutanen Kudancin Kaduna Senatorial District, ina mika gaisuwar taya murna ga uwargidata da sauran wadanda suka samu wannan gagarumar karramawa. Wannan alama ce ta amincewa da jajircewarku wajen hidima da sadaukarwa ga al’umma,” in ji Sanata Katung.

Wannan karramawa ta kara ɗaukaka martabar al’adun Ham tare da bayyana matsayin mata da maza a jagoranci da gina ƙasa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.