Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

An kwato shanu 273, an kama barayin shanu biyu a Kaduna

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta ce ta samu nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da hannu cikin satar shanu a yankin kudancin jihar.

Mai magana da yawun bakin hukumar ’yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan ya tabatar da faruwar Lamarin, a rahoton da ya aika ma manema labarai a ranar laraba a Kaduna.

DSP Hassan, ya ce an samu nasarar kwato shanu 273 da ake zargin an sace su daga wasu guraren a Ishau dake karamar hukumar Piaikoro, border tsakanin jihar Kaduna da Niger.

Ya kara da cewa bincike ya nuna wasu daga cikin shanun sun fito ne daga Jihohin Katsina da Zamfara, inda aka dade ana fama da matsalar satar dabbobi.

ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai domin ganin an shawo kan wannan matsala.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.