Shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Injiniya Bege Joseph Gaiya, ya halarci taron kwanaki biyu kan tsarin sarauta a masarautar Kamuru, da ke yankin Ikulu.
An gudanar da taron ne a fadar sarautar Kamuru daga ranar Asabar 17 zuwa Lahadi 18 ga Mayu, 2025.
Taron ya tattauna tsarin masarautar, iyalan da ke da damar gadon sarauta, da hanyoyin zaben sabon sarki.
An shirya taron ne bisa doka ta jihar Kaduna mai lamba 21 ta shekarar 2021 kan harkokin sarauta.
Masu mukaman gargajiya, masu zaben sarki, da sauran dattawan yankin Ikulu sun halarci taron.
Daraktan Harkokin Iyakoki da Sarauta, Sani Galadima (Dan Majen Godogodo), ya gabatar da bayani kan dokokin sauyin sarauta da rawar da kowane bangare ke takawa.
Inj. Gaiya ya bukaci zaman lafiya da bin doka a duk matakin zaben sabon sarki.
Ya ce: “Wannan taro ya bayar da tsari karara da kowa zai bi, domin a kare martabar gargajiya tare da tabbatar da adalci.”
Gwamnatin Zangon Kataf tana ci gaba da hada kai da sarakunan gargajiya domin karfafa shugabanci a matakin ƙasa da kuma kare al’adu.