Hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kaduna ta fara aikin tabbatar da rajista da biyan haraji ga direbobin Keke Napep a jihar.
Aikin na gudana a wasu kananan hukumomi guda shida: Sabon Gari, Zaria, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Chikun da Igabi.
Manufar ita ce faɗaɗa hanyoyin tara kudin shiga daga harkar sufuri, da kuma tabbatar da cewa duk kekunan haya sun yi rajista kuma suna biyan harajin yau da kullum.
Kafin fara aikin, hukumar ta gana da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri. Ciki har da KASTLEA, KADVS, NURTW, ACCOMORA da sauran su.
Ana amfani da na’urar POS wajen karɓar kuɗin haraji domin sauƙaƙe biyan kuɗi da tabbatar da gaskiya.