Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

A Cikin Watanni 24: Hon. Munira Suleiman Ta Gabatar da Kudirori Hudu A Majalisar Dokokin Kaduna

Published

on

A wani bangare na jajircewar wakilci da kishin kasa, Hon. Munira Suleiman Tanimu, mai wakiltar Lere ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta cimma gagarumar nasara wajen gabatar da kudirori guda hudu cikin watanni 24 da shigarta majalisa.

A ranar Litinin, 6 ga Mayu, 2025, Hon. Munira ta gabatar da sabuwar doka: “Kudiri don kafa Kolejin Kimiyyar Noma da Muhalli ta Jihar Kaduna, Saminaka”. Kudirin ya samu karatun farko cikin nasara.

Ga cikakken jerin kudirorin da ta gabatar:

  1. Gyaran Dokar kashe gobara da kare lafiyar Jama’a ta 2018 – An riga an zartas da ita a matsayin doka.
  2. Dokar Ba Mata Guraben Wakilci a Ofisoshin Gwamnati da Masana’antu (2024) – Ta wuce karatu na biyu, yanzu tana hannun kwamitoci don zurfafa nazari.
  3. Dokar Kafa Hukumar Ayyukan Majalisar Dokokin Kaduna (2025) – Ta samu karatu na biyu kuma tana matakin aiki a kwamitoci.
  4. Kudirin Kafa Kolejin Kimiyyar Noma da Muhalli a Saminaka (2025) – Ya samu karatu na farko a ranar 6 ga Mayu, 2025.

Hon. Munira ta jaddada cewa burinta shi ne ta dora ayyukanta kan inganta rayuwar jama’a, bunkasa ilimi, da baiwa matasa da mata damar da ta dace.

“Ina da yakinin cewa dokoki irin wadannan su ne tushen sauyi mai amfani da dorewa ga Lere ta Gabas da Jihar Kaduna baki ɗaya,” in ji ta.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.