Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin sakin Naira biliyan 3.8 domin biyan kudaden fansho, hakkokin ma’aikatan da suka mutu.
Gwamnan ya yanke wannan hukunci ne bisa tausayi da jin ƙai, bayan korafe-korafen da tsoffin ma’aikata da iyalan wanda suka mutu su ka yi dangane da yadda aikin tantance bayanan fansho ke shafar rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, duk da cewa aikin tantance bayanan fansho yana da matuƙar muhimmanci wajen kawar da masu karɓar fansho na bogi da kuma kare dukiyar jihar, yana da muhimmanci a saukaka wa waɗanda abin ya shafa.
“Wannan gwamnatin na da cikakken himma wajen kula da walwalar tsoffin ma’aikata. Sun sadaukar da rayuwarsu wajen gina jihar Kaduna, don haka wajibi ne a tallafa musu cikin lokacin ritaya,” in ji Gwamna Uba Sani.
Gwamna yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta hanzarta kammala tantancewar domin tabbatar da biyan kudade ba tare da tangarda ba.
Tun bayan hawar Gwamna Uba Sani a watan Mayun 2023, gwamnati sa ta biya Naira biliyan 6.6 a matsayin fansho da sauran hakkokin ma’aikata da suka ritaya da kuma wanda suka rasu.
Ya yabawa tsoffin ma’aikatan bisa haƙuri, fahimta da goyon bayan da suke ba gwamnati, yana mai jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta cikin gaskiya da adalci.