Shugaban ƙaramar hukumar Soba, Hon. Muhammad Shehu Molash, ya karbi bakuncin injiniyar da zai jagoranci gina sabon asibitin kula da marasa lafiya a garin FarinKasa, wanda ke cikin gundumar Richifa a ƙaramar hukumar Soba. Injiniyar, tare da tawagarsa, sun tafi wajen duba wurin da za’a gina asibitin.
A wannan ziyara, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Soba, Hon. Mohammed Garba (Baban-Baba), wanda kuma shine shugaban ƙungiyar majalisar ƙaramar hukumar, da rakiyar Hamza Abdullahi Soba, kakakin Majalisar Kansiloli na ƙaramar hukumar, sun jagoranci injiniyar wajen duba wurin da za’a gina asibitin, wanda zai taimaka wajen saukaka wahalhalu da al’ummar yankin ke fuskanta.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Muhammad Shehu Molash, ya bayyana cewa an kai wannan kokarin ne saboda matsalar da al’ummar garin FarinKasa ke fuskanta wajen samun ingantaccen asibiti a cikin yankin. Wannan ya sa ya kai koke ga Ministan Muhalli na Kasa, Hon. Balarabe Abbas Lawal, wanda ya amince da kokarin sa, sannan ya tura injiniyoyi kai tsaye don duba wurin da za’a gina asibitin.
Injiniyar da zai jagoranci aikin gina asibitin ya tabbatar da cewa za a fara aikin gina asibitin cikin kankanin lokaci, tare da samar da kayayyakin aiki na zamani da kuma horar da ma’aikata ƙwararru domin samar da ingantaccen kulawa ga marasa lafiya.
Shugaban ƙaramar hukumar Soba, Hon. Molash, ya shaida cewa wannan babban aikin na gina asibiti zai amfanar da al’ummar garin FarinKasa da ma sauran yankuna a ƙaramar hukumar, ciki har da al’ummar da za a haifa a nan gaba. Ya kara da cewa wannan aikin na nuni da gwamnatin ƙaramar hukumar Soba na kokarin inganta rayuwar al’umma, musamman wajen samar da ingantaccen kula da lafiya.