A cikin wata gagarumar sauyi a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake tsara hukumar gudanarwar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) Limited, inda ya cire Chief Pius Akinyelure daga matsayin shugaba da kuma Mallam Mele Kolo Kyari daga matsayin Babban Shugaban Gudanarwa (GCEO), tare da sauran mambobin hukumar da aka nada a watan Nuwamba na shekarar 2023.
Sabuwar hukumar mai mambobi 11 za ta kasance karkashin jagorancin Injiniya Bashir Bayo Ojulari a matsayin Babban Shugaban Gudanarwa (GCEO), yayin da Ahmadu Musa Kida zai zama Shugaban Hukumar ba na zartarwa ba. Adedapo Segun, wanda ya maye gurbin Umaru Isa Ajiya a matsayin Babban Jami’in Kudi a bara, shima an nada shi a matsayin mamba a hukumar.
Domin wakiltar shiyyoyin Najeriya guda shida a matsayin mambobin hukumar ba na zartarwa ba, an nada Bello Rabiu (Arewa maso Yamma), Yusuf Usman (Arewa maso Gabas), da Babs Omotowa, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Liquified Natural Gas (NLNG), wanda zai wakilci Arewa ta Tsakiya. Sauran sun hada da Austin Avuru (Kudu maso Kudu), David Ige (Kudu maso Yamma), da Henry Obih (Kudu maso Gabas).
Haka kuma, Mrs. Lydia Shehu Jafiya, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, za ta wakilci ma’aikatar a sabuwar hukumar, yayin da Aminu Said Ahmed zai wakilci Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.
Dukkanin nade-naden sun fara aiki nan take daga ranar 2 ga Afrilu, 2025.
Shugaba Tinubu ya dauki wannan matakin ne bisa dokar Sashe na 59, sakin layi na 2 na Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021. Ya jaddada cewa wannan sauyin yana da nufin inganta gudanarwa, dawo da kwarin gwiwar masu saka jari, bunkasa harkar kayan cikin gida, habaka tattalin arziki, da kuma inganta kasuwancin iskar gas da fadada hanyoyin amfani da shi a Najeriya.
Daga cikin umarnin da Shugaba Tinubu ya baiwa sabuwar hukumar shi ne su gudanar da cikakken bita kan kadarorin NNPC da kuma hadin guiwa da kamfanoni masu zaman kansu, domin tabbatar da cewa ana gudanar da su bisa ingantattun manufofi na bunkasa darajar su.