Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Ta Samu Lambar Girmamawa “Women of Impact”

Published

on

Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, Lokacin Da Take Karban Lambar Girmamawa “The Woman of Impact”.

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta karbi lambar girmamawa ta “Women of Impact” a fannin siyasa da shugabanci a wajen bikin Arise News Gala da aka gudanar a Legas, don tunawa da watan mata na duniya.

A jawabinta, Dr. Hadiza ta godewa Allah da kuma masu shirya wannan karramawa, wato Arise News da ThisDay Group, bisa jajircewarsu wajen girmama mutanen da ke kawo canji mai kyau. Ta nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa damar da ya ba ta don yin hidima, da kuma dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kaduna, musamman mata, da ma’aikatan gwamnati bisa goyon bayan da suka ba ta.

Ta ce wannan lambar yabo alama ce ta ƙoƙarin mutane da ke da hangen nesa wajen kawo ci gaba da daidaito a al’umma. Ta jaddada bukatar ci gaba da shirye-shiryen da ke mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, da habaka tattalin arzikin gajiyayyu, tare da kira ga mata da su ci gaba da tashi tsaye domin tabbatar da cewa ana jin muryarsu a kowanne mataki na rayuwa.

A ƙarshe, Dr. Hadiza ta keɓe wannan lambar yabo ga mata da ‘yan mata na Jihar Kaduna da Arewacin Najeriya gaba ɗaya, tare da jaddada alkawarin ci gaba da aiki tukuru domin kyautata rayuwar al’umma.

Copyright © 2024 kaduna Reports.