Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara domin komawa Majalisar Dattawa a shekarar 2027.
Da yake jawabi a Kaduna yayin bukukuwan Sallah Eid-el-Fitr a gidansa a ranar Lahadi, Shehu Sani ya bayyana shirinsa na siyasa, yana mai cewa: “Duk wani ɗan siyasa da ke son tsayawa takara yana dogaro ne da yanayin siyasar da zai tantance matsayin da za a tsaya. Idan abubuwa suka dace, kuma lissafin siyasa ya ba da dama, zan tsaya takara domin wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa.”
Sanata Shehu Sani ya wakilci Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019. Sai dai rikicinsa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sa ya fice daga jam’iyyar APC, lamarin da ya sa bai iya dawowa majalisa ba.
A cikin jawabinsa na Sallah, Shehu Sani ya bayyana cewa a halin yanzu burinsa na farko shi ne ganin cewa Gwamna Uba Sani ya sake samun nasarar zama gwamna karo na biyu.
“A yanzu dai, burinmu shine mu tabbatar da cewa gwamna mai ci, Uba Sani, ya samu nasarar zarcewa. Za mu yi aiki tukuru da dukkan ƙarfinmu domin cimma wannan buri. Mun san za a fuskanci ƙalubale da adawa, amma mun shirya tsaf don fuskantar kowace irin matsala,” in ji shi.
Shehu Sani ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na Eid-el-Fitr wajen yin addu’a domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Haka kuma, ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wasu farauta a Jihar Edo, yana mai kira ga jami’an tsaro da su kama masu hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
“Idan ‘yan kasa ba za su iya yin tafiya cikin ‘yanci a fadin ƙasa ba, to hakan na nuna cewa ba mu zama ƙasa mai cikakken iko ba. Idan kuma mutane suna ɗaukar doka a hannunsu, to yana nufin babu gwamnati ko wata hukuma mai iko,” in ji shi.
Shehu Sani ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da ke da kishin ƙasa da su ci gaba da aiki tare domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya jaddada cewa hakan ne kadai zai kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban ƙasa, duk da irin ƙalubalen da ake fuskanta.
Bugu da ƙari, ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare haƙƙin dan Adam, musamman haƙƙin rayuwa, domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.